Home Labaru Tsaro: Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin Da ‘Yan Bindiga Su Ka...

Tsaro: Mutane Da Dama Sun Mutu Yayin Da ‘Yan Bindiga Su Ka Faɗa Sansanin Sojoji V

270
0

Wasu ‘yan bindiga da su ka yi kokarin tserewa daga ruwan wutar da sojoji ke yi wa ‘yan ta’adda a jihohin Zamfara da Katsina, sun kwashi kashin su a hannun jami’an soji a ƙauyen Maganda da ke ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja.
Maharan, waɗanda su ka yi kokarin tserewa ta sanannen dajin Allawa, sun faɗa sansanin sojoji, inda su ka fafata na tsawon lokaci.


Rahotnni sun nuna cewa, sojoji sun hallaka ‘yan bindigar da dama, yayin da wasu su ka tsere cikin daji da raunin harbi tattare da su.
Haka kuma, dakarun sojin sun kwato makamai da su ka haɗa da manyan bindigogi masu jigida guda 6, da samfurin AK-47 da dama da kuma buhunan alburusai.

Leave a Reply