Home Labaru Tsaro: Kwamitin Koli Na Shari’a Ya Soki Gwamnatin Tarayya

Tsaro: Kwamitin Koli Na Shari’a Ya Soki Gwamnatin Tarayya

298
0
Dakta Ibrahim Datti Ahmad, Shugaban Kwamitin Koli Na Harkokin Shari'ar Musulunci
Dakta Ibrahim Datti Ahmad, Shugaban Kwamitin Koli Na Harkokin Shari'ar Musulunci

Kwamitin koli na harkokin shari’ar musulunci ya soki salon shugabancin gwamnati tarayya akan sha’anin tsaro, inda ya yi kira ga gwamnati ta sauya salon yakin da take yi ‘yan ta’adda.

Kwamitin ya ce salon da gwamnati ke amfani da shi a bangaren tsaro ba zai samar da zaman lafiyar da ake bukata ba, saboda haka akwai bukatar a duba kwazon shugabannin rundunonin tsaro.

Shugaban kwamitin Dakta Ibrahim Datti Ahmad, ya bayyana  haka a lokacin da yake karantawa manema labarai bayanan bayan taron  kwamitin kan Azumin watan Ramadan a Kaduna, inda ya ce matakan da gwamnati ke dauka ba zasu samar da tsaron da ake bukata ba.

 Dakta Ibrahim Datti ya shawarci gwamnatin tarayya akan ta sauya salon yadda take yaki da kalubalen tsaro ganin yadda lamarin ke naman ya gagari kundila.

Sannan kuma ta sake duba tsare-tsaren da take amfani da su domin ta sauke nauyin da ke kan ta na kare rayuka da dukiyar  jama’a.

Leave a Reply