Home Labaru Tsaro: Kungiyar ‘Yan Wasan Kwaikwayo Za Ta Hada Kai Da Sojojin Wajen...

Tsaro: Kungiyar ‘Yan Wasan Kwaikwayo Za Ta Hada Kai Da Sojojin Wajen Samar Da Tsaro

389
0

Kungiyar ‘yan wasan kwaikwayo ta Nijeriya ta ziyarci babban hafsan sojojin kasa na Nijeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai domin gani an samar da mafita a kan matsalolin tsaro a Nijeriya.

Shugaban kungiyar Steven Eboh ya jagoranci tawagar ‘ya’yan kungiyar zuwa ofishin Buraita da ke Abuja, inda ya ce dalilin ziyarar shine hada gwiwa da rundunar sojin Nijeriya wajen magance kallubalen tsaro da ake fama da shi a sassan kasar’nan.

A karshe Steven Eboh ya jinjina wa Buratai kan nasarar da ya samu na cin galaba a kan mayakan kungiyar Boko Haram.