Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsaro: Kungiyar SERAP Ta Nemi Wasu Bayanai

Kungiyar mai yaki da rashawa da kuma  tabbatar da shugabanci na gari  wato SERAP, ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni 36, su yi wa kasa bayanin abubuwan da su ke yi da kudaden da ake warewa domin inganta tsaro.

Kungiyar ta nemi bayanin kudaden tsaron, ciki har da wani bangare da aka fi sani da Security Vote, a wata takarda ta musamman da ta aike wa shugaban kasa da gwamnonin sa.

Takardar wacce ke dauke da sa hannun mataimakin shugaban kungiyar, Kolawale Oluwadare, ta ce sashi na 14, da kuma kashi na 2 na kundin tsarin mulkin kasa na cewa tsaron rayukan al’ummar kasa da dukiyoyinsu sun tahalaka ne kacokan akan gwamnati.

Kungiyar SERAP ta ce dole ne a dauki matakin magance matsalar cikin sauri kafin lokacin da za a kafa sabuwar gwamnati nan da lokaci kadan.

Amma ministan wasanni da matasa, Barista Solomon Dalung, ya ce batun kudin kulawa da tsaro abu ne da kundin tsarin mulki ya tanada, kuma ba bu wanda zai iya yin wani abu akai, sai  an yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima.

Exit mobile version