Home Labaru Tsaro: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Samu Hatsari A Jihar Katsina

Tsaro: Jirgin Rundunar Sojin Sama Ya Samu Hatsari A Jihar Katsina

452
0

Jirgin rundunar sojin saman Najeriya ya samu hatsari yayin sauka a jihar katsina bayan ya dawo daga aikin da su keyi na yakar ‘yan bindigar da suka addabi yankin areawa maso yammacin kasar nan a karkashin shirin rundunar sojin Najeriya na OPERATION SHARAN DAJI da yake gudana a wannan yankin.

Air marshal Sadique Abubakar, Hafsan Rundunar Sojin Sama Na Kasa

Lamarin ya faru ne yau laraba misalin karfe 3:30 na ranar yau a babban filin saukan jiragen sama dake jihar katsina.

A bayanan da da mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya Ibikunle Daramola ya fitar ya nuna cewa “ba a samu ararar rayuka ba kuma a nan take hafsan rundunar sojin sama na kasa Air marshal Sadique Abubakar ya bada umurnin kafa kwamitin binciken musabbabin faruwar wannan al’amarin.

Leave a Reply