Home Labaru Tsaro: Jami’an Tsaro Sun Hallaka Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar...

Tsaro: Jami’an Tsaro Sun Hallaka Gungun Masu Garkuwa Da Mutane A Jihar Kogi

240
0

Hadakar rundunar jami’an tsaron Nijeriya da su ka hada da Sojoji da ‘yan sanda, sun yi rawar gani yayin wani artabu da su ka yi da gungun ‘yan bindiga a jihar Kogi.

Jami’an tsaron, tare da taimakon mafarauta sun samu nasarar hallaka ‘yan bindiga uku, sannan sun jikkata wasu biyu kamar yadda kaakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Kogi ya tabbatar.

Kakakin rundunar ASP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce lamarin ya auku ne a ranar 11 ga watan Satumba, bayan wasu ‘yan bindiga 5 sun yi awon gaba da wasu mutane 6 a kan hanyar Iyamoye da ke karamar hukumar Ijumu.

Daga cikin mutanen da ‘yan bindigan su ka sata kuwa akwai Cif Ganiyu Popoola, da kannen sa biyu maza da mace daya da mijin ta, sai kuma wani mutum da ba a bayyana sunan sa ba.

Bayan ‘yan bindigar sun kwace kudaden su ne su ka tasa keyar su zuwa mafakarsu da ke kungurmin daji, amma bayan wasu ‘yan sa’o’i sun saki Ganiyu Popoola da dan uwasa Sule, da nufin su nemo kudin fansar sauran mutanen da ke hannun su.