Home Labaru Tsaro: Hukumar DSS Ta Sha Alwashin Hukunta Masu Yada Kalaman Batanci A...

Tsaro: Hukumar DSS Ta Sha Alwashin Hukunta Masu Yada Kalaman Batanci A Yanar Bizo

379
0

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS, ta ce ta kama wasu ‘yan Nijeriya da ke amfani da shafin sada zumunta su na yada kalaman da ka iya tada rikici a kasa.

Kakakin hukumar Afunanya, ya ce matakin da su ka dauka ya zama dole, saboda wasu marasa kishin kasa su na wallafa bayyanan da za su iya kawo rikici a kasa

Afunanya ya bada tabbacin cewa, hukumar za ta cigaba da kamawa tare da hukunta masu aikata irin wadannan rubuce-rubuce a kafafen sada zumunta na zamani.

Hukumar, ta kuma gargadi ‘yan Nijeriya su yi takatsantsan da irin abubuwan da su ke wallafawa a shafukan su na sada zumunta, saboda ta fara farautar mutanen da ke wallafa abubuwan da ka iya janyo rikici a kasa.

Leave a Reply