Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tsaro: Garkuwa Da Kashe-Kashe Sun Ragu A Fadin Nijeriya – Sufeto Janar

Mohammed Adamu, Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Mohammed Adamu, Shugaban rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu, ya ce kashe-kashe da sauran ayyukan karya dokokin tsaron kasa sun ragu matuka a watannin karshen wannan shekara.

Ya ce hakan ya faru ne sakamakon taron tattauna zaman lafiya da gwamnatin tarayya ta bijiro da shi, ya na mai cewa, idan aka kwatanta yanzu da kuma baya za a fahimci cewa tashe-tashen hankila sun ragu sosai.

Mohammed Adamu, ya ce ba su dade da kammala zaman taron samar da zaman lafiya ba, inda su ka fahimci cewa batun tsaro a Nijeriya ya na kara inganta sosai, kuma sun fahimci cewa sata da garkuwa da mutane da hare-haren ‘yan bindiga sun ragu.

Shugaban ‘yan sandan ya bayyana wa manema labarai haka ne a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, inda ya ce tayin afuwar da gwamnati ta yi wa masu garkuwa da mutane ta kara karfafa tsaro a Nijeriya.

Exit mobile version