Home Labaru Tsaro: Dakarun Soji Sun Ceto Mutum 34 Da Aka Yi Garkuwa Da...

Tsaro: Dakarun Soji Sun Ceto Mutum 34 Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Benue

236
0

Shelkwatar tsaro ta kasa ta ce rundunar sojin Najeriya ta ceto mutu 34 da aka yi garkuwa da su, ta damke wasu da ake zargi da laifin garkuwa da mutane tare da samo miyagun makamai a jihar Benue.

Shugaban bangaren yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche

Shugaban bangaren yada labarai na rundunar, Manjo Janar John Enenche, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar a Abuja, inda ya ce nasarorin da aka samu sun biyo bayan bayanan sirrin da ake samu  akan inda miyagun masu garkuwa da mutanen suke.

Ya ce, dakarun rundunar sun yi misayar wuta da ‘yan ta’addan wanda hakan ya kai ga kashe wani mutum daya mai suna Zwa Ikyegh, wanda bincike ya nuna shi ne shugaban kungiyar.

Ya ce babu kakkautawa zakakuran sojin suka garzaya inda lamarin ya faru tare da kama mutum biyu da ake zargi.