Home Labaru Tsaro: Buhari Ya Tura Tawagar Manyan Hafsoshin Soja Da ‘Yan Sanda Jihar...

Tsaro: Buhari Ya Tura Tawagar Manyan Hafsoshin Soja Da ‘Yan Sanda Jihar Katsina

1335
0

Wasu manya hukumomin tsaron Nijeriya sun isa Katsina a wani yunkuri na gudanar da bincike tare da samun bayanai a kan barnar da ‘yan bindiga suke aiwatarwa a wasu kananan hukumomin jihar.

Tawaga ta isa jihar Katsina ne bisa umarnin shugaban kasa Muhammadu Buhari, wanda ya bukaci shugaban ‘yan sandan nijeriya Adamu Muhammed da shugaban hafsoshin sojin Nijeriya, Janar Abayomi Olanishokin su je jihar domin samo wasu bayanai.

Idan dai ba a manta ba, a ranar Larabar da ta gabata ma shugaban kasa Buhari ya gayyaci gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari zuwa fadar shugaban kasa domin su tattauna game da matsalar tsaro a jihar, inda suka kwashe wasu awanni suna ganawa, wanda daga bisani tawagar manyan jami’an soji da ‘yan sanda su ka isa jihar.

‘Yan tawagar da suka isa jihar sun hada da mataimakin shugaban ‘yan sanda Abdulmajid Ali da kwamandan rundunar soji ta 17 da ke Katsina Birgediya L Omoniyi da wasu manyan hafsoshi daga rundunar sojan kasa da ta sama da kuma hukumar tsaro ta farin kaya.

Sai dai tawagar bata bayyana wa manema labarai iya kwanakin da za ta yi a jihar ta na gudanar da wannan bincike kamar yadda shugaban kasa Buhari ya umarta ba.

Leave a Reply