Hukumar ‘yan sandan Nijeriya ta gabatar da wasu masu garkuwa da mutane 40 ga manema labarai a hedkwatan hukumar SARS da ke Abuja.
Daga cikin wadannan aka gabatar, akwai 13 da su ka yi garkuwa da magajin garin Daura kusan watanni 3 da suka gabata.
Karanta Wannan: Tsaro: ‘Yan Sanda Sun Kama ’Yan Tada-Zaune-Tsaye 90 A Kano
Kakakin hukumar DCP Frank Mba, ya ce an tattara wadannan ‘yan bindigar ne a wurare daban-daban a jihohin Kano da Katsina.
Daga cikin abubuwan da aka samu a hannun su sun hada da bama-bamai da bindiga kirar AK47 guda 20 da kwamfutoci da sinadarin hada bama-bamai da kayan sojoji da wasu muggan makami.
Shugaban wadanda sukayi garkuwa da magajin garin Dauran, ya bayyana sunansa a matsayin Yusuf Dahiru ya kuma labartawa manema labarai cewa, sun yanke shawarar garkuwa da shi ne domin fito da wasu abokan aikin su da ke hannun jami’an tsaro.
Dahiru ya kuma bayyana manema labarai cewa, duk da cewa sun tsareshi na tsawon kwanaki 60, ba su ci mutuncin sa ba kuma sun yi matukar girmama shi, amma wani daga cikin su ya ce, sun aikata aika-aikan ne domin samun kudin dala miliyan talatin a matsayin fansa, tunda babban mutum ne suka sace.