Home Labaru Tsaka Mai Wuya: Kotu Ta Karbi Sabbin Shaidu A Kan Tuhumar Da...

Tsaka Mai Wuya: Kotu Ta Karbi Sabbin Shaidu A Kan Tuhumar Da EFCC Ke Yi Wa Nyako

347
0

Wata kotun tarayya da ke zama a Abuja, ta karbi karin wasu takardu a matsayin shaida, a ci-gaba da tuhumar zargin badakalar naira biliyan 29 da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako.

An dai gurfanar da Nyako tare da dan sa Sanata Abdul-Aziz Nyako da Abubakar Aliyu da Zulkifikk Abba bisa tuhumar su da hada baki domin aikata sata da cin amanar aiki da safarar kudi.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ce ta gurfanar da Nyako da dan sa Sanata Abdul-Aziz tare da ragowar mutanen biyu.

Lauya mai kare wadanda ake tuhuma Ibrahim Isiaku, ya roki kotu ta dage sauraron karar domin su yi nazarin shaidun da Odofin ya gabatar a gaban kotun.

Alkalin kotun mai shari’a Okon Abang, ya daga sauraren karar zuwa ranar 10 ga watan Afrilu, domin lauyan da ke kare wadanda ake kara ya gabatar da tambayoyi ga Odofin.

Leave a Reply