Home Labarai Tsadar Rayuwa: Fasa Rumbunan Ajiye Abinci Babban Laifi Ne-Minista

Tsadar Rayuwa: Fasa Rumbunan Ajiye Abinci Babban Laifi Ne-Minista

44
0

Ƙaramar ministar Abuja ta bayyana ayyukan fasa rumbun ajiye
abinci da wasu mutane suka yi a birnin da cewa babban laifi ne.


Dr. Mariya Mahmoud ta bayyana hakan ne bayan kai ziyarar gani da ido domin shaida irin ɓarnar da aka yi a wajen ajiye abincin da aka tatuke.
A shafinta na X ta wallafa cewa ta je rumbun ajiye abinci a Gwagwa-Tasha domin tantance irin ɓarnar da zauna-gari-banza suka yi, inda ta ce wannan abin ya wuce yunwa, babban laifi ne.


Mariya, ta ce abinda ta gani abu ne mara daɗi, yanayi ne da wasu zauna-gari-banza suka wawushe duka hatsin da sauran
kayan abinci da ke wurin.


Wani ɗankasuwan da BBC ta zanta da shi a unguwar Karmo ya ce mutane sun wawashe masa kayan abinci a wurin ajiyar kayan
dake Karmo.


Mutumin ya ce lamarin da ya faru a ranar Lahadi, ya janyo masa asarar sama da naira miliyan 100.

Leave a Reply