Maniyyata aikin Hajji sun shiga jimami da rudu bayan da
Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da karin kudin
aikin Hajjin bana daga Naira miliyan hudu da doriya zuwa Naira
miliyan 8.3.
A baya Hukumar NAHCON ta buƙaci maniyyata daga jihohin Kudu su biya Naira miliyan 4 da dubu 899, yayin da maniyyatan Arewa za su biya Naira miliyan 4 da dubu 699.
Sai dai Hukumar NAHCON ta sanar da cewa an kara kudin kujerar da Naira miliyan daya da dubu 900, saboda matsalar karyewar darajar Naira, inda yanzu kuɗin suka koma Naira miliyan 6 da dubu 800 kan kujera, ga wanda ya yi ajiya ko ya biya kudinsa tuntuni.
Sannan wadanda za su yi sabon biya kudin ya haura Naira miliyan 8, kamar yadda mai magana da yawun hukumar, Hajiya Farima Sanda Usara ta fadi a wata sanarwar a Yammacin Lahadin, tana mai cewa lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana, Dala ba ta yi tashin da ta yi ba a yanzu.
Wannan mataki ya dama lissafin maniyyata da dama inda wasu suka fara yunkurin neman Hukumar NAHCON ta dawo musu da kudadensu na aikin Hajjin da suka biya.
Malaman addini da kungiyoyin farar hula, sun bukaci Shugaba Kasa Bola Ahmed Tinubu ya ceto maniyyatan kasar nan, la’akari da matsin tattalin arzikin da ake ciki.