Home Home Tonon Silili: CBN Ya Kasa Yin Bayanin Yadda Aka Yi Bindiga Da...

Tonon Silili: CBN Ya Kasa Yin Bayanin Yadda Aka Yi Bindiga Da Dala Biliyan 4.5

111
0

Wani Bincike da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya gudanar ya nuna cewa, Babban Bankin Nijeriya ya kasa yin bayanin yadda aka yi da wata Dala biliyan 4 da rabi da aka kamfata daga Asusun Kuɗaɗen Waje tsakanin shekara ta 2018 da 2019.

Rahoton shekara-shekara na Ofishin Akanta Janar a kan yadda ma’aikatu da cibiyoyi da hukumomin gwamnatin tarayya su ka kashe kuɗaɗen su, ya nuna cewa an rasa yadda bankin CBN ya yi da kuɗaɗen, kuma babu su babu dalilin su.

Salwantar kuɗaɗen dai ta faru ne, lokacin mulkin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ƙarƙashin tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, Godwin Emefiele.

Rahoton ya ce, adadin kuɗaɗe ne ajiye har Dala Biliyan 42 da miliyan 594 da dubu 842 da 852 a cikin shekara ta 2018, amma abin mamaki, a cikin watan Disamba na shekara ta 2019 sai kuɗaɗen su ka koma Dala biliyan 38 da miliyan 92 da dubu 720.

Wato a ƙididdige dai an kafci Dala biliyan 4 da Miliyan 502 da dubu 122 da 652, kuma an rasa yadda aka yi da kuɗaɗen, don haka Akanta Janar ta Tarayya Shaakaa Chira, ta nemi bankin CBN ya fito da sahihan bayanai ko kuma a fito da kuɗaɗen.

Leave a Reply