Home Labaru Tona Asiri- Rashin Gaskiya Ne Ya Hana Aikin Wuta A Mambila –...

Tona Asiri- Rashin Gaskiya Ne Ya Hana Aikin Wuta A Mambila – Ministan Lantarki

2110
0
Sale Mamman, Ministan Lantarki
Sale Mamman, Ministan Lantarki

Ministan lantarki Injiniya Sale Mamman, ya ce nan bada jimawa bane za a fara aikin tashar lantarki ta Mambila dake jihar Taraba, sabanin maganganun da ake yi a baya cewa aiki ya yi nisa.

A wata hirar sa da kafar BBC, ministan ya ce sabanin da ake samu tsakanin gwamnatin tarayya da kuma kamfanonin rarraba lantarki na daya daga cikin abubuwan da suka janyo tsaiko a aikin samar da lantarki a Najeriya.

Ya ce babbar matsalar da ta dabaibaye fannin wutar lantarki ita ce matsalar cin hanci da rashawa inda ya ce cin amana da rashin gaskiya ne yake kara gurgunta harkar wutar lantarkin.

Ministan ya ce sau da dama wasu za su zo su karbi kudi kamar za su yi aiki da gaske amma daga baya sai kaga an yi karkatar da kudin.

Ya yi zargin cewa wasu daga cikin shugabannin baya sun sa son rai game da aikin lantarkin, wanda hakan ya ja ba a samun isashshen lantarki.

Ministan ya yi alkawari kafin shekara ta 2023 za a samar da kusan mega watts dubu 20 na lantarkin ta yadda ‘yan Najeriya za su rika samun wuta babu katsewa.

Leave a Reply