Home Labaru Tona Asiri: An Gano Wasu Kamfanoni Da Ake Zargi Da Rashawa A...

Tona Asiri: An Gano Wasu Kamfanoni Da Ake Zargi Da Rashawa A Nijeriya

348
0
Kasashen Afrika Na Kashe Dala Biliyan 50 Kan Sayen Abinci-AFDB
Kasashen Afrika Na Kashe Dala Biliyan 50 Kan Sayen Abinci-AFDB

Bankin Duniya tare da babban bankin ci gaban Afirka, AfDB, sun Tona asirin  sake wasu manyan kamfanonin gine-gine na kasar Chana da akaita rashawa.

Ana zargin kamfanonin su shida da tabka almundana  da zamba a cikin aminci a cikin kasar nan. Kamfanonin sune, China Railway Construction (International) Nigeria Company Limited, China Railway 18th Bureau Nigeria Engineering Company Limited, CCECC Nigeria Lekki (FTA) Company Limited.

Sauran sunhada da, kamfanin CCECC Nigeria Railway Company Limited, CRCC Petroleum & Gas Company Limited sai kuma CCECC Nigeria Company Limited.

Manyan bankunan biyu sun ce wadannan kamfanoni da ke aikin kwangiloli masu tarin yawa a wurare daban-daban a fadin kasar nan, sun sabawa yarjejeniya da sharuddan  ayyukan kwangila da aka gindaya a fadmdin duniya.

Makamancin wannan hukunci ya rataya a kan wasu masu ayyukan kwangila a fadin duniya biyo bayan alumundahar  ta rashin gaskiya da saba alkawali da suka yi a wurare daban daban a fadin duniya.

Kafar yada labarai ta  Premium Times ce  ta ruwaito, wadannan kamfanoni da aka kama dumu-dumu da laifi a yanzu, ba su hadar da wasu manyan kamfanoni shida ba na kasar China da bankin duniya ya tona asirin su harda kuma   shafa masu kashin Kaji na zamba da rashawa.

Bugu da kari,  kamfanoni na taka rawar gani a fannoni daban-daban wajen bunkasa tattalin arzikin kasar nan a lokacin  da suke gudanar da ayyukan kwangiloli da dama na biliyoyin nairori da suka shafi yi wa gwamnatin tarayya da kuma ta jihohi aikace-aikace da gine-ginen hanyoyi, gidaje, wutar lantarki, ma’adanan ruwa, gadaje na sama da na Nijeriya.

Amma bankin duniya ya haramta su daga cikin kamfanonin da ya bai wa lasisin aiwatar da duk wata kwangila da ta kai ta kudaden ciwo bashi daga bankin, inda aka dakatar da su har na tsawon shekara guda.

Leave a Reply