Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tirkashi: Ƴan Najeriya Na Cikin Waɗanda Suka Fi Fama Da Ciwon Mantuwa A Duniya – Bincike

Ciwon mantuwa da ake kira 'dementia' na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil'adama.

Ciwon mantuwa da ake kira ‘dementia’ na ɗaya daga cikin cututukan da ke barazana ga lafiyar bil’adama.

Kungiyar da ta gudanar da binciken mai suna Alzheimer’s Disease International ta ce sama da mutum miliyan 40 ke fama da cutar a duniya ba tare da sun sani ba.

Binciken ya kiyasta cewa kashi 75 cikin 100 na ɗauke da cutar ba tare da sun sani ba, kuma wadanan alkaluma sun fi yawa a kasashen Najeriya da Indiya da kashi 90 cikin 100.

Rahoton ya ƙunshi kundin nazari daga manyan masana 50 a faɗin duniya game da cutar.

Shugabar kungiyar, Paolo Barbarino ta ce tsangwama da rashin wayewa da rashin bincike sun taka rawa wajen samun karuwar masu ɗauke da cutar.

Hukumar Lafiya ta WHO ta kiyasta cewa adadin mutanen da ke dauke da cutar a duniya za su haura miliyan 130 kafin shekara ta 2050.

 

Exit mobile version