Home Home Tinubu Ya Gabatar Da Cikon Sunayen Mutanen Da Yake Son Naɗawa Ministoci

Tinubu Ya Gabatar Da Cikon Sunayen Mutanen Da Yake Son Naɗawa Ministoci

47
0

Shugaban ma’aikatan fadar shugaba kasa Femi Gbajabiamila, ya gabatar wa majalisar dattawa jerin sunaye na biyu na mutanen da shugaba Tinubu ke neman amincewar ta domin naɗa su ministoci.

Femi Gbajabiamila ya miƙa sunayen ne ga shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio, a daidai lokacin da majalisar ke tantance wasu daga cikin mutanen da ke cikin jerin farko na sunayen da aka gabatar mata.

Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana ƙarin sunayen mutane 19 da Shugaba Bola Tinubu ya aika masu domin naɗa su ministoci.

Daga cikin jerin sunayen kuwa, akwai tsofaffin gwamnonin da su ka hada da Bello Matawalle na jihar Zamfara, da Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma Gboyega Oyetola na jihar Osun.

Sauran tsofaffin gwamnonin su hada da Ibrahim Geidam na jihar Yobe, da kuma  Simon Lalong na Jihar Filato.

Leave a Reply