Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Ya Fadawa Gwamnoni 36 Su Aiko Masa Sunayen Mutanen Da Zai Ba Mukami

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga
Gwamnonin jihohi su kai sunayen mutanen da su ka cancanta
a ba mukamai.

Rahotanni dai sun ruwaito cewa, tuni shugaba Tinubu ya jingine batun jam’iyya ya nemi kowane Gwamna ya kai ma shi sunayen mutanen da su ka cancanta a ba mukamai.

Wata majiya ta ce, za a duba wadanda su ka dace a ba mukamai ne a majalisun da ke kula da hukumomi da ma’aikatu da cibiyoyin gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar gwamnoni AbdulRahman AbdulRazaq ya bayyana haka, jim kadan bayan wani taron gaugawan da su ka yi a Abuja, inda ya ce kungiyar ta yaba wa gwamnatin Tinubu game da yadda ta nuna jagoranci ta ba kowane Gwamna dama duk da sabani da bambancin jam’iyya.

Exit mobile version