Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Ya Bukaci Hukumomi Da Su Yi Musayar Bayanan Sirri Domin Yaki Da Ta’Addanci

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nuna wa jami’an tsaro
da na leken asiri muhimmancin musayar bayanan sirri a
tsakanin su, inda ya ce boye irin wadannan bayanai na iya
kawo cikas wajen yaki da ta’addanci.

Tinubu ya bayyana haka ne, bayan wata ziyarar aiki da ya kai sabon ofishin mai bada shawara a kan harkokin tsaro da gine- gine a Cibiyar yaki da ta’addanci ta kasa da ke Abuja.

Yayin da yake lura da kokarin da aka nuna wajen yakar ta’addanci da na’urorin zamani a cibiyoyin biyu, shugaba Tinubu ya ce gwamnatin shi ta fahimci cewa idan har za a samu farfado da tattalin arziki da wadata da ci-gaba, ya kamata a ba da fifiko ga bangaren tsaro.

Ya ce abin farin ciki ne sosai ganin cewa ana samun kayan aiki, ya nai cewa ba Nijeriya ce kadai ke fama da ta’addanci ba a fadin duniya, don haka dole ne a yake shi a kauda shi gaba daya.

Exit mobile version