Home Labaru Tinubu Ya Ƙalubalanci Atiku Kan Yaɗa Shari’Ar Zaɓen Shugaban Ƙasa Kai-Tsaye

Tinubu Ya Ƙalubalanci Atiku Kan Yaɗa Shari’Ar Zaɓen Shugaban Ƙasa Kai-Tsaye

54
0

Zaɓaɓɓen Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya nuna
adawa da buƙatar da ɗan takarar Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar
PDP Atiku Abubakar ya yi na watsa shirye-shiryen kai tsaye a
kan yadda shari’ar zaɓen ke gudana.

A wani martanin da aka gabatar ta hannun tawagar lauyoyin su, Tinubu da Kashim Shettima sun ce buƙatar ta cin zarafin kotu ce, don haka su ka bukaci Kotun ta yi watsi da bukatar, su na masu cewa agajin da masu neman zaɓen su ka nema bai kai yadda kotu za ta iya ba.

Baya ga bayyana aikace-aikacen a matsayin rashin gaskiya, sun ce kotun ba gidan wasan kwaikwayo ba ce ko gidan kashe ahu domin nishaɗin jama’a.

Tinubu da Kashim Shettima sun yi zargin cewa, Atiku Abubakar da jam’iyyar PDP sun kasa janyo hankalin kotu a kan yadda kotuna su ka bada umarnin gudanar da shari’ar.

Leave a Reply