Home Home Tinubu Orders Review Of Governing Boards Of Tertiary Institutions

Tinubu Orders Review Of Governing Boards Of Tertiary Institutions

72
0
Ilimi: Babu Ranar Bude Makarantu Duk Da An Sassauta Takunkumi - Minista
Ilimi: Babu Ranar Bude Makarantu Duk Da An Sassauta Takunkumi - Minista

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin sake yin dubi ga kwamitocin gudanarwa na manyan makarantun da aka nada a baya-bayan nan.

Ya ba da umarnin ne domin yin abin da ya kamata kafin kaddamar da taron bita da aka shiryawa ‘yan kwamitocin ranar 31 ga watan Mayun nan da muke ciki.

Mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

A kwanakin baya ne ma’aikatar ilimi ta tarayya ta fitar da sunayen wadanda aka zaba a matsayin shugabanni, da ‘yan kwamitin gudanarwa na jami’o’i da manyan makarantu da kwalejojin ilimi.

Sai dai kuma martanin da jama’a suka yi ya nuna cewa nade-naden da aka yi bai yi daidai da tsarin tarayya ba domin wasu jihohin sun samu nadi daya ne, yayin da wasu kuma suka samu da yawa.

Ya ce bitar za ta kuma yi la’akari da yaduwar kasa da kuma tabbatar da cewa kowane bangare na kasar nan ya samu wakilci.

Leave a Reply