Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tinubu Bai Bude Iyakokin Nijeriya Ba -Kwastam

Hukumar Hana Fasa Kauri ta Kasa, ta ce har yanzu shugaba Tinubu bai sake bude dukkan iyakokin Nijeriya da tsohuwar gwamnatin Buhari ta rufe ba.

Idan dai za a iya tunawa, a shekara ta 2019 ne Buhari ya rufe dukkan iyakokin Nijeriya domin hana shigo da wasu kaya ba bisa ka’ida ba, wadanda su ka hada da shinkafa da bindigogi da sauran su.

Bayan shekaru biyu, gwamnatin Buhari ta sake bude kadan daga cikin iyakokin, wasu kuma sun kasance a rufe duk da kokawar da ‘yan Nijeriya su ka yi.

Kwanakin baya ne aka rika yada wani tsohon faifan bidiyo a shafukan sada zumunta, inda aka ga shugaban hukumar Kwastam na jihar Ogun Bamidele Makinde ya bude shingen da ke kan iyakar Idiroko da Jamhuriyar Benin.

Exit mobile version