Home Labarai Tinubu Ba Zai Yi Murabus Ba, Inji Ministan Yaɗa Labarai

Tinubu Ba Zai Yi Murabus Ba, Inji Ministan Yaɗa Labarai

36
0

Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa kiran da Ƙungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP ta yi wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na ya yi murabus ba komai ba ne illa wani yunƙuri na karkatar da hankalin jama’a daga mutanen da ya kamata su shagaltu da tallafa wa ƙoƙarin shugaban ƙasa na kawo wa al’ummar Nijeriya agajin gyaran tattalin arziki.

A cewarsa, bai kamata PDP da gwamnonin ta su riƙa nema, ta hanyar tsoratarwa, abin da su ka kasa cimmawa ta hanyar dimokiraɗiyya tun cikin shekarar 2015.

A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara game da aikin jarida, Rabi’u Ibrahim, ya bayar, Idris ya ce: bai kamata waɗanda su ka gaza kawo sauyi a lokacin da su ka samu dama mai tsawo ba su nemi katsewa ko karkatar da hankalin masu aiki kan manufar shugaban ƙasa da ‘yan Nijeriya su ka zaɓe su don aiwatarwa ba.

A karshe ya kara da cewa, Gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, tun da aka kafa ta, ta ba da tallafin kuɗi ga dukkan gwamnatocin jihohi, ba tare da la’akari da ɓangaranci ba.

Leave a Reply