Home Labarai Tinubu : Ba Ɗabi’Ata Ba Ce Ɗora Laifi Kan Gwamnatoci Da Suka...

Tinubu : Ba Ɗabi’Ata Ba Ce Ɗora Laifi Kan Gwamnatoci Da Suka Gabata

99
0

Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce ba halinsa ba ne ya ɗora wa gwamnatocin da suka shuɗe laifi kan taɓarɓarewar tattalin arziki da kuma rashin tsaro  da Najeriya ke fama da shi.

Shugaban Tinubu ya ce ya himmatu wajen ɗaukar matakan da suka dace na sake farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar da kuma tsayawa kan turbar da ta dace don samun ci gaba.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabi a wani biki kan magance ƙarancin abinci a Minna, babban birnin jihar Neja.

Sai dai Tinubu, wanda ya karɓi ragamar mulki daga hannun Buhari a watan Mayun bara, ya ce damuwarsa ba wai ya zargi gwamnatocin da suka gabata ba, illa ɓullo da tsare-tsaren da suka dace domin ɗora ƙasar kan turbar ci gaba.

Da yawa daga cikin mukarraban gwamnatin Tinubu ciki har da ministan kuɗi Wale Edun, sun ɗora laifin matsalolin tattalin arziki da kuma tsaro da ƙasar ke fuskanta a kan gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.

Najeriya dai na fama da matsalar garkuwa da mutane don neman kuɗin fansa, hauhawar farashin kayayyaki, tashin farashin dala, matsalar tattalin arziki da kuma tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.

Leave a Reply