Home Labaru Tilas A Naɗa Wike Minista A Gwamnatin APC – Fayose

Tilas A Naɗa Wike Minista A Gwamnatin APC – Fayose

66
0

Tsohon Gwamna jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya ce ya na sa
ran za ta ɓaci matuka matsawar Shugaba Bola Tinubu ya ƙi
naɗa Nysom Wike a matsayin Minista.

Ayodele Fayose, ya ce dole Shugaba Tinubu ya bayyana godiyar sa ga Gwamnonin G5 na jam’iyyar PDP, waɗanda su ka tsaya domin tabbatar da adalci a zaɓen ɗan kudancin Nijeriya a matsayin shugaban kasa.

A wata tattaunawa da ya yi da Gidan Talabijin na Channels, Fayose ya bayyana yadda Nysom Wike ya jajirce domin tabbatar da ganin ɗan takarar shugaban kasa daga kudancin Nijeriya ya yi galaba a kan Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP daga yankin Arewa.

Da ya ke zantawa da manema labarai a fadar shugaban kasa jim kadan bayan ganawa da shugaba Tinu, Fayose ba za su fice daga jam’iyyar PDP ba har abada, amma kuma dole su yaba wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Leave a Reply