Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tawagar ECOWAS Ta Bar Nijar Ba Tare Da Ganin Jagoran Juyin Mulki Ba

Tawagar da kungiyar ECOWAS ta tura, ta bar Nijar ba tare da ganawa da jagoran sojojin da su ka yi juyin mulki ba.

Rahotanni sun ce, Tawagar ta isa birnin Yamai, sai dai ba ta kwana ba kamar yadda aka tsara, kuma ba ta gana da jagoran juyin mulkin Janar Abdourahamane Tchiani ba, kuma ba ta hadu da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum ba.

Tsohon Shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ne ya jagoranci tawagar, kuma an tsara za ta gana da Tchiani domin gabatar masa da bukatar kungiyar ECOWAS.

Shugaba Tinubu dai ya ce ECOWAS za ta yi bakin kokarin ta wajen warware matsalar cikin ruwan sanyi, amma za ta iya amfani da karfin soji a matsayin mataki na karshe, yayin jagoran juyin mulkin Nijar ya yi gargadi cewa a shirye su ke su maida martani mai karfi.

Exit mobile version