Home Labarai Tattaunawar Nukiliya: Kasashen G7 Sun Gargadi Iran

Tattaunawar Nukiliya: Kasashen G7 Sun Gargadi Iran

147
0
Ministocin kasashen G7 wato ƙasa bakwai mafiya girman tattalin arziki na shirin yi wa Iran gargadin cewa lokaci na kure mata kan ci gaba da tattauna shirinta na Nukiliya.

Ministocin kasashen G7 wato ƙasa bakwai mafiya girman tattalin arziki  na shirin yi wa Iran gargadin cewa lokaci na kure mata kan ci gaba da tattauna shirinta na Nukiliya.

Masu shiga tsakani daga Amurka za su sake komawa birnin Vienna na Austria don ci gaba da zama kan batun.

Wakilin BBC ya ce a halin da ake ciki babu tabbas ko gwamnati a Tehran na da zimmar kawo karshen wannan tirka-tirka.

Amma Shugaba Raisi na Iran ya kafe cewa kasar sa da gaske take, kuma suna fatan a cimma abin da ake so bayan tattaunawar a wannan karon.

Leave a Reply