Bankin Duniya ya yi hasashen samun habbakar tattalin arzikin Nijeriya da akalla kashi 2 da rabi cikin 100 a shekara ta 2022, sama da kashi 2.4 da bankin ya yi hasashe a shekara ta 2021.
Alkaluman da bankin ya fitar a kan hasashen tattalin arzikin
kasashe, ya ce tattalin arzikin Nijeriya zai rika habbaka shekara
bayan shekara, wanda ke da nasaba da tashin farashin man fetur
da kudaden da ta ke samu a bangaren sadarwa da hukumomin
kudi.
Nijeriya, dai ita ce mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika da
ta dogara a kan man fetur wajen samun kudaden shiga,
alkaluman da Bankin Duniya ya fitar sun nuna cewa bayan
samun karuwar tattalin arziki da kashi 2 da rabi a shekara ta
2022 zai sake karuwa da kusan kashi 3 a shekara ta 2023.
Bankin ya kara da cewa, wasu daga cikin dalilan da za su
taimaka wa tattalin arzikin Nijeriya sun hada da matakin
kungiyar kasashe masu albarakatun man fetur OPEC, na rage
yawan man da manyan kasashe masu arzikin man fetur ke
fitarwa, da wasu sabbin tsare-tsare da za su taimaka wa kananan
kasashen kungiyar.