Home Labarai Tattalin Arziki: Yadda Gwamnoni 13 Suka Ci Bashin Kusan Naira Biliyan 250...

Tattalin Arziki: Yadda Gwamnoni 13 Suka Ci Bashin Kusan Naira Biliyan 250 A Wata Shida

255
0

Hukumar kula da basussuka ta kasa ta ce a cikin wata shida
sababbin gwamnonin jihohi 13 na ƙasar ciki har da Kano, da
Zamfara, da Katsina sun ci bashin naira biliyan 226 daga masu
bayar da bashi a ciki da wajen ƙasar.


Gwamnonin jihohin na daga cikin gwamnoni 16 na ƙasar da suka ci bashin bayan rantsar da su a kan mulki a cikin watan
Mayun 2023, inda hukumar kula da basukan ƙasa ta ce ta haɗa al’ƙaluman ne bayan jumlar lissafin da suka yi kan farashin dala a kan naira 889.


Hakan dai na ƙunshe a cikin wani rohoto da ta wallafa a shafinta na internet, inda ta ce an ci bashin ne a tsakanin 30 ga watan Yunin da 30 ga watan Disamba na 2023.


Rohoton da hukumar kula da basukan ta kasa ta wallafa ya nuna cewar gwamnoni 16 na ƙasar sun ƙara yawan bashin cikin gida da ake bin jihohinsu da naira biliyan 509, yayin da na ƙetare ya kai naira biliyan 243 da miliyan 95, da kusan dala miliyan 300 kwatankwacin naira biliyan 265 da miliyan 37.

Dr Aminu Achida masanin tattalin arzki na Jami’ar Usman Dan Fodiyo da ke Sokoto ya ce hakan alama ce da ke nuna irin halin da Najeriya ke ciki, wanda ka iya sanya ƙasar cikin yanayi na kasa biyan albashi da kuma kasa gudanar da gwamnati saboda rashin kuɗi.

Leave a Reply