Home Labaru Kasuwanci Tattalin Arziki: Masu Zuba Jari Sun Ja Baya Daga Nijeriya – MDD

Tattalin Arziki: Masu Zuba Jari Sun Ja Baya Daga Nijeriya – MDD

463
0

Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya ce, adadin jarin da ‘yan kasuwa na kasashen waje ke zubawa a Nijeriya ya ragu da kashi 42 cikin dari.

Rahoton ya ce, masu zuba jarin dai sun ji takaicin yadda rikici ya barke tsakanin gwamnati da kamfanin sadarwa na MTN a kan batun fitar da ribar da kamfanin ya samu daga Nijeriya.

Ya ce jarin dala biliyan biyu kawai Nijeriyar ta samu a shekarar da ta gabata, da ikirarin da hukumomin Nijeriya ke yi ewa su na kyautata yanayin kasuwanci domin jan hankalin masu zuba jari.

Koma-bayan da Nijeriya ta samu dai ya zo ne, duk da cewa nahiyar Afirka ta samu karuwar zuba jari daga kasashen ketare da kashi 13 cikin dari, abin da ya kawo karshen koma-bayan da aka shafe shekaru biyu ana samu.

Rahoton ya kara da cewa, ayyukan hakar sabbin ma’adinai da man fetur da kafa cibiyar kudi da kuma aiwatar da shirin cinikayya maras shinge tsakanin kasashen zai iya kara adadin jarin da ake zubawa a nahiyar.