Home Labaru Tattalin Arziki: Falana Ya Soki Tsohuwar Gwamnatin Ibrahim Babangida

Tattalin Arziki: Falana Ya Soki Tsohuwar Gwamnatin Ibrahim Babangida

290
0

Babban Lauya Femi Falana, ya zargi tsohuwar gwamnatin Janar Ibrahim Babangida da hannu wajen jefa Nijeriya cikin mummunan halin da ta shiga ta fuskar tattalin arziki.

Femi Falana, ya ce tsarin tada komadar tattalin arziki na SAP da gwamnatin Babangida ta kawo a shekara ta 1986 ne ya sa tattalin Nijeriya ya tabarbare sanidiyyar saida wa Attajirai kasar nan.

Lauyan, ya kuma yi watsi da maganar yaki da cin hanci da rashawa da jam’iyyar APC ta ke da’awa, inda ya ce gwamnonin APC ba da gaske su ke yi wajen yakar satar kudin jama’a ba.

Falana ya kara da cewa, bai kamata a bar wannan yaki a kan gwamnatin tarayya kwai ba, domin a halin yanzu Kano ce kawai jihar da ke da hukumar yaki da cin hanci da rashawa a dukkan jihohi 20 na jam’iyyar APC.

A karshe ya ba shugaba Buhari shawara da cewa, ya raba kudin da ya karbo har Naira Biliyan 1 daga hannun Barayin gwamnati ga kananan hukumomi domin kawo ci-gaba a yankuna karkara.