Hukumar kiyeye haddura ta kasa FRSC ta ce akalla ma’aikatan ta 2000 ne ke jibge a dandalin rantsar da shugaban kasa Buhari na Eagle Square da ke Abuja.
Wani babban jami’in hukumar da ke kula da titunan Nijeriya, Gora Wobin ya ce, za a sa ma’aikatan su lura hanyoyi a yayin da ake sake rantsar da shugaban kasa Buhari.
Gora Wobin ya bayyana haka ne a lokacin da yak e zantawa da manema labarai a Abuja, inda ya kara da cewa sun shirya ma’aikatan su tsaf domin gyara hanya da kuma kula da cinkoso a lokacin rantsarwar.
Ya ce duk motar da aka gani kusa da wajen taron, za a dauke ta a matsayin barazana, saboda haka dole ne a gudanar da bincike a kan ta kafin a janye ta.