Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dawo Nijeriya, bayan halartar taron kungiyar kasashen Afrika karo na 12 a birnin Niamey na jumhuriyar Nijar.
Rahotanni sun ce jirgin Shugaban kasar da ke dauke da shugaba Buhari da wasu mukarraban sa ya isa filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da misalin karfe 1:25 na ranar Litinin din nan.
A wajen taron dai, Nijeriya da Benin sun sanya hannu a kan wata yarjejeniyar kulla huldar kasuwanci a gaban shugabannin kasashen da ke halartar taron.
Mahalarta taron dai, sun tafa wa shugaba Buhari da takwaran sa na kasar Benin Patrice Talon, yayin da su ka sa hannu a kan takardun yarjejeniyar, a hedikwatar jamhuriyar Nijar da ke birnin Niamey, inda za a kafa helkwatar cibiyar kasuwanci da yarjejeniyar ta samar.