Home Labaru Kasuwanci Tara: Kamfanin MTN Ya Biya Naira Biliyan 330

Tara: Kamfanin MTN Ya Biya Naira Biliyan 330

517
0

Kamfanin sadarwa na MTN mallakin Afrika ta Kudu, ya biya kashin karshe na tarar da gwamnatin tarayya ta yanke masa, a dalilin saba ka’idar rashin yiwa miliyoyin layukan sa rijista, ko kuma katse layukan da ba’a yiwa rijistar ba.

A kashin karshe dai kamfanin na MTN ya biya gwamnatin Najeriya Naira miliyan dubu 55, abinda ya bashi damar kammala biyan tarar Naira miliyan dubu 330 da hukumar kula da harkokin sadarwar ta Najeriya NCC ta yanke masa a shekarar 2016.

Da fari dai a watan Oktoban 2015 hukumar ta NCC ta yanke wa MTN biyan tarar Naira miliyan sau miliyan 1 da doriya ne, saboda laifin kin katse layukan sa akalla miliyan 5 da ba a yiwa rijista ba, duk da cewa gwamnati ta ba ilahirin kamfanonin sadarwar da ke kasar umarnin yin hakan, to amma daga bisani a 2016 aka sassauta tarar zuwa Naira miliyan dubu 330.

Leave a Reply