Home Labaru Ilimi Tantancewa: Katsina Za Ta Yi Wa Shugabanni Da Malaman Sakandire Jarabawa

Tantancewa: Katsina Za Ta Yi Wa Shugabanni Da Malaman Sakandire Jarabawa

30
0
c06f4fcd535ca28829fb62cbb3828094 e1727251969781.webp
c06f4fcd535ca28829fb62cbb3828094 e1727251969781.webp

Gwamnatin jihar Katsina ta bayyana shirin ta na gudanar shirya jarabawar tantancewa ga dukkan shugabanni da mataimakan shugabanni, da malaman makarantun sakandire na jihar.

Gwamnatin ta ce za a shirya jarrabawar ne da nufin taimaka wa gwamnati wajen sake nada mukamai da kuma tabbatar da matakin da ya dace ga shugabancin makarantu, da inganta kwazo da ingantaccen jagoranci a makarantu.

Kwamishiniyar ilimi a matakin farko da sakandire a jihar, Zainab Musawa ce ta bayyana haka a Katsina yayin da take yi wa manema labarai karin haske,

kan yadda daliban jihar suka samu sakamako mai kyau bayan kammala jarabawar (NECO) na shekarar 2024.

Zainab Musawa ta bayyana cewa, ma’aikatar ta kuma shirya sake dawo da azuzuwan bada horo na tilas ga duk daliban da suka kusa kammala makarantar sakandire domin kara musu kaimi musamman a fannin Lissafi da Turanci.

Yayin da take jaddada kwazon dalibai a jarabawar NECO, kwamishiniyar ta ce, jihar ta zo ta shida a yawan daliban da suka fita da (credit 5) zuwa sama da haka,

Da suka hada da Lissafi da Ingilishi, wanda ta bayyana a matsayin babban nasara.

Ta kara da cewa, wannan gagarumar nasara da daliban suka yi, nuni ne na gaskiya da irin jajircewar da gwamnati ta yi wajen kawo sauyi a fannin ilimi,

Da samar da kayayyakin koyarwa, da kayayyakin aiki, da kuma daukar fiye da malamai 7,000 aiki tun lokacin da gwamnati mai ci a jihar ta zo.

Leave a Reply