Home Labaru Tallafin Mai: Majalisar Dattawa Ta Amince A Biya Bashin Naira Miliyan Dubu...

Tallafin Mai: Majalisar Dattawa Ta Amince A Biya Bashin Naira Miliyan Dubu 129

352
0

Majalisar Dattawa ta amince a biya bashin Naira miliyan dubu 129 a matsayin kudin tallafi ga kamfanonin Mai guda 67, lamarin da ke nuna cewa daga watan Yuli na shekarar da ta gabata zuwa yau, gwamnatin tarayya ta biya kamfanonin sama da Naira biliyan 545.
Majalisar ta amince ta biya kudaden ne, bisa shawarar da kwamitin kula da albarkatun man fetur a karkashin shugabancin Sanata Kabiru Marafa ya gabatar.

Wannan dai na nufin cewa, Nijeriya ta kashe sama da naira tiriliyan 11 domin biyan kudin tallafin man fetur a cikin shekaru 6 da su ka gabata, kamar dai yadda kwamitin harkokin Mai na majalisar dattawa ya byyana.

Leave a Reply