Home Labaru Tallafi: Sarkin Makkah Ya Talalawa Marayu 2,073 A Jihar Kebbi

Tallafi: Sarkin Makkah Ya Talalawa Marayu 2,073 A Jihar Kebbi

1077
0
Dakta Abdul Aziz Bin Ahmad Al-Sarhan, Babban Sakataren Kungiyar Bada Agaji Na Musulunci
Dakta Abdul Aziz Bin Ahmad Al-Sarhan, Babban Sakataren Kungiyar Bada Agaji Na Musulunci

Akalla marayu dubu biyu da saba’in da uku ne suka amfana da wani shirin bada tallafin kudi da gwamnatin kasar Saudiyya a karkashin Sarki Salman ta bayar a jihar Kebbi.

Babban sakataren kungiyar bada agaji na musulunci, Dakta Abdul Aziz bin Ahmad Al-Sarhan da gwamna Atiku Bagudu ne suka kaddamar da shirin, inda suka  zabo marayu daga garuruwa guda takwas na jihar Kebbi, daga ciki har da Birnin Kebbi, inda daga nan ne aka fara aikin rabon kudin.

Sauran yankunan da suka amfana da shirin sun hada da Gulumbe, Gwandu, Argungu, Jega, Koko, Shanga da kuma Yauri.

Wakilin sakataren kungiyar Tahiru Baba Ibrahim, ya ce  za’a bada kudin ne bisa dadewar rajistan da marayun suka yi a kungiyar, saboda akwai wasu marayun da suka yi rajista da kungiyar tun shekaru uku da suka gabata, yayin da wasu kuma shekaru biyu da suka gabata, wasu kuma kasa da haka.  Shi ma da yake na sa jawabin, gwamnan jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu, ya ce jin dadinsa da wannan tallafi, inda ya ce baya ga jihar Borno da Yobe, jihar Kebbi ce ta uku wajen yawan yan gudun hijira, kuma ita ke da yawan almajirai saboda kusancinta da wasu kasashen Afrika.

Leave a Reply