Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Tallafi: Japan Ta Ba Nijeriya Taimako Kudade Don Farfado Da Yankin Arewa Maso Gabas

Gwamnatin kasar Japan ta tallafa wa Nijeriya da kyautar kudi
dala miliyan daya da dubu dari biyar domin sake gina yankin
Arewa maso gabas da ayyukan kungiyar Boko Haram ya lalata.
Kasar Japan ta bayyana haka ne a ranar Talatar da ta gabata,
inda ta ce za a kashe wadannan kudade ne a karkashin tsarin
cigaba na majalisar dinkin duniya UNDP da yanzu haka ya ke
gudana a Nijeriya.
Jakadan kasar Japan a Nijeriya Shigeru Umetsu ya ce wadannan
kudade za su karkata ne wajen kulawa tare da taimaka wa
mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa a jahohin Borno,
Adamawa da Yobe domin su farfado daga mummunan halin da
yakin ye je fasu ciki.

Umetsu ya ce, wadannan kudade wasu bangare ne na ayyukan
jin kai da gwamnatin kasar Japan ke gudanarwa a yankin Arewa
maso gabas, wanda ayyukan suka hada da gyaran gine-gine da
daukar ‘yan gudun hijira kimanin 2000 aikin wucin gadi.
Haka kuma, an bawa manoma fiye da 4,000 tallafin kayan aiki,
kama taimaka wa masu kananan sana’o’i 1000 da tallafin jari,
domin ganin su samun kudaden shiga don gudanar da karkokin
su cikin jin dadi da walwala.

Exit mobile version