Home Labaru Taliban Ta Yi Magana Kan Al-Qaeda

Taliban Ta Yi Magana Kan Al-Qaeda

254
0

Mai magana da yawun ƙungiyar Taliban, ya yi watsi da rahotannin Majalisar Dinkin Duniya da ke nuna cewa kungiyar mayaƙan Al-Qaeda na gudanar da harakokin su a Afghanistan, inda ya kira iƙirarin cewa ba ya da tushe.

Da ya ke magana da wata kafar labarai ta Pakistan, Sohail Shaheen ya ce Taliban za ta girmama yarjejeniyar da ta ƙulla a Doha, wadda ta ƙulla shekarar da ta gabata da Amurka a kan daƙile amfani da Afghanistan a matsayin sansanin kai hare-hare kan wasu kasashe.

Ya kuma yi watsi da rahotannin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa akwai mayaƙan Al-Qaeda a kusan rabin lardunan Afghanistan.

Ya ce Wadannan rahotannin sun dogara ne da bayanan karya da abokan hamayya su ka bada, ya na mai cewa, nan gaba, jami’an tsaro da na leƙen asiri na Taliban za su kara himma wajen sa ido a kan barazanar.