Tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha, ya zargi Emeka gwamnan Imo Ihedioha da sabawa dokar aiki ta hanyar ta sa Iyalinsa a gaba.
Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake magana da manema labarai, , inda ya roki Emeka Ihedioha da ya kyale Yaransa da kuma Matarsa da ya hana sakat.
Rikicin Okorocha da sabon gwamnan na jihar Imo ya dauki wani salo tun bayan da ya karbi mulki, bayan Okorocha ya yi kokarin kakaba Surukinsa domin ya gajesa a zaben da ya gabata, amma hakan bai yiwu ba.
Gwamna Emeka Ihedioha, ya fara rusa wasu ayyuka da gwamnatin Rochas Okorocha ta yi, bayan da ya hau kan kujerar mulki.
Tsohon gwamnan ya na zargin Sakataren gwamnatin jihar, da kuma gwamna ma ci da muzgunuwa mai dakinsa da kuma ‘Diyarsa.