Babbar kotun tarayya da ke Kano, ta umarci hukumar zabe ta karbe shaidar cin zaben da ta ba tsohon mai ba shugaban kasa shawara a kan harkokin majalisar wakilai Kawu Sumaila, cewa ba shi ya cancanta ya zama dan majalisar wakilai na mazabar da ya ke wakilta a jihar Kano ba.
Da ya ke zartar da hukuncin, Alkali Lewis Allagoa, ya ce jam’iyyar APC ba ta yi daidai ba wajen musanya ainihin dan takarar da aka yi zaben fidda gwani da shi wato Abdur-Rahman Dambazau.
Lauyan Dambazau Nuraini Jimoh, ya ce tun farko Kawu Sumaila bai tsaya takarar kujerar dan majalisar Wakilai ba, ya nemi kujerar sanata ne su ka fafata da Sanata Kabiru Gaya, inda Kabiru Gaya ya yi nasara a zaben fidda gwani a wancan lokaci.
Tuni dai kotun ta umarci hukumar Zabe ta gaggauta kwace shahadar da ta ba wa Kawu sumaila ta ba Dambazau cewa shi ne ainihin dan majalisar da aka zaba.