Home Labaru Take Hakkin Bil’adama: Amnesty Ta Gargadi Gwamnatin Buhari Kan Kisan Jama’a

Take Hakkin Bil’adama: Amnesty Ta Gargadi Gwamnatin Buhari Kan Kisan Jama’a

312
0

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin tarayya ta kawo karshen take hakkin dan Adam a Najeriya.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Amnesty ta ce wa’adin mulkin Buhari na farko an kashe ‘yan Shi’a sama da 350 da kuma masu fafutikar kafa kasar Biafra 150 da aka kashe tsakanin 2015 zuwa 2016.


Kungiyar ta ce harkokin tsaro a Najeriya na kara tabarbarewa inda ta ce, a Zamfara an kashe daruruwan mutane sannan cikin shekara uku daga 2015 alkalummanta sun nuna kusan mutum 4,000 aka kashe a rikicin makiyaya da manoma.


Kungiyar ta fadi wasu jerin bukatu da suka shafi hakkin bil-Adama wadanda ta ce ya kamata hukumomin Najeriya su mayar da hankali a kai yayin da aka shiga sabon wa’adin mulki a kasar.


Cikin bukatun da kungiyar ta ce idan aka aiwatar da su za su taimaka wajen kyautata hakkin bil-Adama a kasar, sun hada da kare hakkin mata da kananan yara da kuma soke hukuncin kisa.


Hukumomin Najeriya dai sun dade suna yin watsi da rahoton Amnesty, kuma zuwa yanzu babu wani martani da ya fito daga bangaren gwamnatin Najeriya game da sanarwar ta Amnesty.