Rundunar sojin kasa ta Najeriya ta kai samame babban ofishin hukumar Hisbah ta jahar Jigawa dake garin Dutse da nufin kwato wasu dimbin kwalaben giya da jami’an hukumar suka kwace a wasu gidajen shan barasa dake jihar.
Babban kwamandan Hisbah na jahar Jigawa, Malam Ibrahim Dahiru Garki, ne ya bayyana haka a Dutse, inda ya ce jami’an Hisbah sun dakile yunkurin Sojojin.
Garki, ya ce jami’an Hisbah sun bi wasu gidajen shan barasa dake garin Dutse, inda suka kwace kwalaben haramtattun giya katan 70, amma wasu sojoji su 7 suka dira ofishin Hisban da nufin kwace kwalaben giyan da karfi da tsiya.
Ya ce da samun labarin ne suka yi gaugawar tuntubar shugaban hukumar tsaro ta DSS da kuma kwamishinan ‘yan sandan jahar, wadanda suka aika da jami’ansu zuwa ofishin Hisban, amma sojojin sun juya ba tare da daukan komai ba.
Kwamandan Operation Salama da ke garin Dutse, Laftanar M.I Ikemba, ya ce sharri ake yi wa dakarun Soja, babu wasu Sojoji suka shiga ofishin Hisbah da nufin kwatan kwalaben giya.
You must log in to post a comment.