Home Labaru Kasuwanci Takaddama:’Yan Sanda Sun Rufe Ofishin O’pay A Jihar Kano

Takaddama:’Yan Sanda Sun Rufe Ofishin O’pay A Jihar Kano

1093
0

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen jihar Kano ta rufe ofishin da ‘Yan adaidaita-Sahu ke biyan kudi ta kafar yanar gizo ko kuma Intanet mai suna OPAY.

Rundunar ta rufe ofishin ne yayin wani sumame da ‘yan sanda suka kai saboda rashin bin dokokin gwamnati da kamfanin baya yi, inda suka isa ofishin kamfanin dake Lodge road a Kano.

‘Yan sanda sun umurci dukkan ma’aikatan kamfanin da masu Adaidaita-Sahu dake wurin su fice, inda su kayi barazanar kama dukkan wanda bai yi biyaya ga umurnin su ba.

Wani wanda abin ya faru a idonsa ya shaidawa manema labarai cewar masu Adaidaita-Sahun suna shirin biyan kudin cinikin su kayi ne ‘yan sandan suka daran masu.

Mai magana da yawun ‘yan sanda na jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce gwamnatin jihar Kano ce ta ba rundunar umurnin rufe wurin, saboda kamfanin na Opay ya saba wasu dokoki da gwamnatin jihar ta kafa masa.