Home Labaru Ilimi Takaddama:Kungiyar ASUU Na Shirin Komawa Yajin-Aiki Bayan Ta Ba Gwamnati Wa’Adi.

Takaddama:Kungiyar ASUU Na Shirin Komawa Yajin-Aiki Bayan Ta Ba Gwamnati Wa’Adi.

132
0

Kungiyar malaman jami’o’i  ta ASUU sun bayyana shirinsu na shiga wani sabon yajin-aiki.

Wani rahoto ya ce  kungiyar ASUU za ta shiga yajin-aiki ne a dalilin zargin da ta ke yi wa gwamnati na kin cika alkawarun da ta dauka.

 Kungiyar ASUU ta ba gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari zuwa karshen wata, wato yau Talata, 31 ga watan Agusta, 2021, ta tuntube ta, ko a rufe jami’o’i.

Shugaban kungiyar ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya bayyana hakan a lokacin da ta zanta da shi, inda ya ce wa’adin da malaman jami’o’in suka ba gwamnatin tarayya zai kare, idan ba a cimma matsaya ba, za a iya daina karantar da dalibai.

Farfesa Osodeke, ya ce kungiyar su ba za ta ji nauyin shiga wani yajin-aiki domin nuna wa gwamnatin tarayya bacin ranta kan saba alkawari ba.