Home Labaru Takaddama: Sarakunan Zamfara Sun Kalubalanci Ministan Tsaro Mansur Dan Ali

Takaddama: Sarakunan Zamfara Sun Kalubalanci Ministan Tsaro Mansur Dan Ali

186
0

Sarakunan Zamfara sun kalubalanci ministan tsaro Mansur Dan Ali, da ya bayyana sunayen sarakunan da ya ce su na hada baki da ‘yan ta’addan da ke kai hare-hare a jihar Zamfara su na azabtar da mutane.

Shugaban majalisar Sarakunan jihar Zamfara Mai martaba sarkin Anka Alhaji Attahiru Muhammad ya bayyana matsayar sarakunan, bayan wani taron gaugawa da su ka yi a garin Gusau.

Sarkin Anka, ya ce rashin bayyana sunayen sarakunan zai nuna cewa ministan ba gaskiya ya fada ba, kuma ya yi hakan ne domin ya ci mutuncin sarakunan jihar.

Haka kuma, sarakunan sun koka a kan yadda jiragen saman soji ke kai hare-hare a kan mutane ba maboyar mahara ba.