Home Labaru Takaddama: Minista Ya Dakatar Da Daukar Sabbin Ma’aikata A Hukumar NDDC

Takaddama: Minista Ya Dakatar Da Daukar Sabbin Ma’aikata A Hukumar NDDC

431
0
Godswill Akpabio, Ministan Harkokin Neja Delta Sanata
Godswill Akpabio, Ministan Harkokin Neja Delta Sanata

Gwamnatin Tarayya ba bada umurnin dakatar da daukar ma’aikata a hukumar raya yankin Neja Delta nan take.

Ministan harkokin Neja Delta Sanata Godswill Akpabio ya bada umurnin, inda ya ce a dakatar da bada takardar daukar aiki da sauran harkokin da su ka shafi daukar aiki a hukumar.

Sanawar, wadda babbar sakatariyar yada labarai ta ministan Anietie Ekong ta fitar, ta ce Akpabio ya bada umurnin ne a cikin wata wasika da sakataren dindindin na ma’aikatar yankin Neja Delta Didi Walson-Jack ya aike wa mukadashin daraktan hukumar Dakta Akwagaga Enyia.

Ya ce umurnin da ministan ya bada, hukumar ba ta da kudin daukar sabbin ma’aikata, don haka ta koma yadda ta ke gudanar da al’amurran ta kamar da, yayin da ya umurci a ba shi rahoton wadanda aka dauka aiki.

Idan dai ba a manta ba, a baya Ministan ya ce za a gudanar da bincike a kan duk kudaden da su ka shiga ma’aikatar, wadanda aka kiyasta sun kai sama da naira tiriliyan 2 domin gano yadda aka kashe su.

Leave a Reply