Mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa shiyyar Arewacin Nijeriya Lawal Shu’aibu, ya ce ba zai bayyana a gaban kwamitin jam’iyyar APC da aka bukaci ya gurfana a gaban shi ba.
Idan dai ba a manta ba, Kwanakin baya Lawal shu’aibu ya bukaci Adams Oshiomhole ya sauka daga kujerar shugabancin jam’iyyar, inda ya ce Oshiomhole na da hannu a badakalar rasa jihar Zamfara da APC ta yi.
Sakamakon wadannan kalamai da Lawal ya yi ne jam’iyyar ta nada kwamiti, domin ya zo gabanta ya fadi dalilan da su ka sa ya jefi Oshiomole da munanan kalamai.
Sai dai Lawal ya ce ko nada wannan kwamiti da aka yi ba a bi dokar jam’iyyar ba, domin doka ba ta ba jam’iyyar da shi kan sa shugaban ta zai jagoranci zaman da aka ce wai an nada domin ta bincike shi.
Ya ce a yanzu dai ya na sanar da duniya da ita kan ta jam’iyyar APC cewa ba zai bayyana a gaban kwamitin ba